'Yan sanda 35 sun bace a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin Liman-kara ya sa rundunar 'yan sandan Najeriya ta bada umarni a tsaurara tsaro a sansanonin 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta ce har yanzu ba ta gano jami'anta 35 ba, cikin wadanda suka watse a lokacin harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a sansanin horas da 'yan sandan kwantar da tarzoma da ke garin Liman Kara a jihar Borno.

Kakakin rundunar, Mr. Emmanuel Ojukwu ya ce an gano 'yan sanda da dama da suke a sansanin horaswar a lokacin harin, kuma ana ci gaba da neman ragowar.

Sai dai ya ce yanzu ba za a iya yanke hukunci akan ko 'yan kungiyar Boko Haram sunyi garkuwa da jami'an 'yan sandan ba.

Mr. Ojukwu ya ce mai yiwuwa an kashe wasu daga cikin su, amma har yanzu ba a samu gawarwakin su ba, wasu kuma kila sun gudu neman tsira lokacin harin.

Garin Liman Kara da ke cikin karamar hukumar Gwoza, wadda ta yi fama da hare-haren 'yan kungiyar ta Boko Haram a baya-bayan nan, ya na daya daga cikin garuruwan da ake samun masu kaura zuwa wasu wurare saboda hare-haren kungiyar.