Za a daure duk wanda ya boye mai Ebola

Hakkin mallakar hoto

Majalisar dokokin Saliyo ta zartar da wani kudirin doka wanda ya tanadi hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari ga duk mutumin da aka samu ya boye wani wanda yake dauke da cutar Ebola.

Wani jami'in gwamnati yace matakin na da nufin dakile yada cutar ce a tsakanin al'umma.

A wani bangare kuma kasar Ivory Coast ta rufe iyakarta da kasashen Libya da Guinea. Gwamnatin Ivory Coast ta ce tana tunkarar yaduwar cutar daga kasashe biyu da ke makwabtaka da ita.

Ivory Coast din dai ita ce kasar Afrika ta baya bayan nan da ta takaita zirga zirga duk da gargadin da hukumar lafiya ta duniya ta yi cewa hakan na iya haifar da karancin abinci a kasashen da lamarin ya shafa.

Mutane fiye da 1,300 ne suka rasu a sakamakon cutar Ebola a kasashen Liberia da Guinea da Saliyo. An kuma sami mutum biyar da suka rasu a Najeriya.

Karin bayani