Ebola ta bulla a Jamhuriyar Congo

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Mutane goma sha-daya yanzu haka na kwance a asibiti

Hukumomi a Jumhuriyar Demokradiyyar Congo sun ce bayan wani bincike, an gano cewar wata annoba ta wani zazzabi da ta barke - Ebola ce.

Ministan lafiya na kasar Felix Numbi ya gaya ma BBC cewar gwaje-gwajen da aka yi ma wasu mutane biyu sun tabbatar da cutar a lardin Equateur wurinda mutane goma sha-ukku suka rigaya suka mutu.

Zuwa yanzu, mutane goma sha-ukku sun mutu.

Akwai mutane goma sha-daya da yanzu haka suke kwance asibiti, kuma daga cikinsu 5 ma'aikatan lafiyar ne.

To, amma Ministan ya ce mutanen sun mutu ne a wani wuri dake kebe, akwai kuma alamun cewa ita wannan cutar na'uin ta ya bambanta da ta yammacin Afrika.

Dr Numbi yace an rigaya an killace wuraren da za a ajiye majityyata cutar don shawo kan ta.