Yahudawa sun yi tir da Isra'ila

Hakkin mallakar hoto
Image caption Yahudawan da suka tsira daga kisan 'yan Nazi sun kuma soki Amurka akan goyon bayan Isra'ila

Sama da yahudawa 300 da suka tsira daga kisan kiyashin 'yan Nazi da kuma 'ya'ya da jikokin wasu da suka tsiran sun fitar da wata sanarwa, inda suke Allah-wadai da abin da suka kira kisan kare dangin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa.

Sanarwar wadda aka buga a jaridar New York Times ta Amurka, ta yi kira da a kawo karshen datse hanyoyin shiga Gaza da Isra'ila ta yi, kuma a kauracewa Isra'ilan.

Wadanda suka sanya hannu a sanarwar sun nuna damuwarsu kan, abin da suka kira, cin mutunci da wulakanci da nuna wariyar da ake yi wa Falasdinawa a yankunan Isra'ila.

Yahudawan sun kuma soki Amurka kan daukar nauyin da take yi na hare haren soji da Isra'ila ke kai wa a Gaza.