Saudiyya: Taron ministocin larabawa kan IS

Taron ministocin kasashen larabawa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Taron ministocin kasashen larabawa

Kasar Saudiyya na karbar bakuncin wani taro a birnin Jeddah na ministocin harkokin waje daga kasashen larabawa.

Kasashen sun hada Masar da Jordan da Qatar da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Kasashen za su tattauna martaninsu dangane da bullar mayakan jihadin kasar musulunci a Syria da kuma Iraqi.

Ministocin sun fito ne daga kasashen kungiyar aminan Syria wadda ta nuna adawa da gwamnatin Syria ta shugaba Bashar al Assad.

Ma'aikatar harkokin wajen Masar ta ce ana matukar bukatar samun masalaha ta siyasa fiye da kowane lokaci domin warware rikicin.

Karin bayani