Sojoji sun yi watsi da ikirarin Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Boko Haram ta kwace garin Gwoza na jahar Borno

Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi watsi da ikirarin da shugaban kungiyar Boko Haram Abubkar Shekau ya yi na cewa garin Gwoza da 'yan kungiyar suka kwace daga hannun dakarun Najeriya, a yanzu ba ya karkashin Najeriya, ya koma karkashin daular musulunci.

Kakakin hedikwatar tsaron, Manjo janar Chris Olukolade ya ce 'yanci da daukacin farfajiyar kasar Najeriya na nan yadda yake.

Kuma ya ce ba za a amince da duk wani ikirari na wata kungiyar ta'adanci dake cewa ta mamaye wani bangare na kasar ba.

'Ba zan iya tabbatar da sahihancin bidiyon ba'

Gwamna Kashin Shetiima a cikin sanarwar da ya fitar ya ce ba zai iya yin tsokaci game da sahihancin bidiyon ba ko kuma akasin haka.

Ya ce zai barwa jami'an tsaro su gudanar da bincikensu.

Gwamnan ya ce kuma ba zai iya bayyana irin matakan da hukumomin tsaro suke dauka a Gwoza ba, koma a wani bangare na jahar Borno.

Amma ya ce yana tabbatarwa da al'ummar jahar Bornon dama sauran jama'a cewa gwamnatin jahar tana baiwa jam'an tsaron da aka tura goyan bayan da suke bukata a kokarin da suke na dakile ayyukan tada kayar baya.