'Salon yaki ne zuwan Sojin Nigeria Kamaru'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rundunar sojojin Kamaru ce ta bayyana sanarwar tsallaka kan iyakar sojojin daga Nijeriya zuwa kasar bayan fafatawa da Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce shigar sojojin kasar su 480 cikin jamhuriyar Kamaru wata dabarar yaki ce.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriyar ta fitar a ranar Litinin.

Ta kara da cewa saboda dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ya sa dole aka kwance damarar sojin Najeriya, saboda su tabbatar wa Kamaru cewa ba su da wata mummunar manufa gare ta.

A cewar sanarwar komai ya daidaita kuma sojojin da suka tseren na kan hanyarsu ta koma wa Najeriya.