Kungiyar Musulmi ta soki kafa daular Musulunci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Muric ta ce mafarki ne shelar kafa daular musulunci a gwoza tun da akwai kafuwar yardaddun Hukumomi

Wata kungiyar kare hakkin al'ummar Musulmi a Nijeriya MURIC, ta yi watsi da shelar jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da ke bayyana Gwoza a matsayin daular musulunci.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, MURIC ta kafa hujja da ayar alkur'ani, inda ta ce Musulunci ya yi umarni da yin biyayya ga Hukumomin kasa, amma Boko Haram ta bijire.

Ta ce yayin da neman kowanne ilmi ya zama ginshikin rayuwa a musulunci, kungiyar ta haramta ilimin Boko, a lokaci guda kuma ta hana mata neman ilimi, duk da karfafa musu gwiwar yin haka da hadisin Annabi (SAW) ya yi.

Sanarwar ta ce shelar Boko Haram sanarwa ce ta a-ware, wadda ba za a amince da ita ba, ta ce jazaman ne a karbo garin Gwoza cikin 'yan kwanaki.

Kungiyar kare hakkin musulmin ta yi jan hankali a kan fatawar Babban malamin Saudiyya da kungiyar hada kan musulmin duniya da ke haramta kungiyar Boko Haram.