An fafata tsakanin dakarun Ukraine da na Rasha

kan iyakar Ukraine Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption kan iyakar Ukraine

Kasar Ukraine ta ce dakarunta sun fafata da ayarin wasu motoci masu sulke da tankokin yaki wadanda suka kutsa daga Russia zuwa yankin gabashin kasar da ke hannun 'yan tawaye.

Kakakin rundunar sojin Andriy Lysenko ya ce ayarin ya kutsa ne ta lardin Doneshk, kodayake an dakatar da su.

Ya bayyana kutsen a matsayin wani yunkuri na bude sabon babin rikici tsakanin Ukraine da Russia.