An saci bayanai a cibiyoyin kamfanin UPS

Jiragen sama na kamfanin UPS Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jiragen sama na kamfanin UPS

An saci bayanan sirri na mutane da dama da suka yi hulda da rassan kamfanin kai sakonni na Amurka UPS.

Satar bayanan wadda ta shafi rassa 51 a jihohi 24 ta fallasa sunayen abokan huddar da adireshinsu na kai sakonni da adireshinsu na email da bayanan katinsu na banki.

Kamfanin yace, an cire tsarin da masu7 satar bayanan suka saka, don haka a yanzu ba za a fuskanci wata matsala ba.

A ranar litinin, wani reshe na asibitin Amurka ya yi koken cewa, wasu sun yi kutse a shafukkansu na hulda da mutane.

An saci bayanan majiyyata kimanin miliyan hudu da dubu dari biyar.

A makon da ya wuce, wani babban kantin sayar da kayan abinci na Amurka SuperValu ya yi koken cewa wasu, sun yi kutse a shafinsu, sun saci bayanai na abokan huddarsu.

Kamfanin na UPS wanda aka kafa a matsayin kamfanin kai sakonni a shekara ta 1907, wanda ya zamo babban kamfanin kai sakonni, yana da rassa sama da 4,450 a Amurka.

Kowanne reshe dai kusan yana zaman kansa ne, kuma shine ke da alhakin kafawa da kula da duk wasu tsare-tsarensa na hanyar sadarwa ta internet.

Kamfanin na UPS ya gano ana satar bayanansa ne bayan da gwamnatin Amurka ta tsegunta masa, kuma lamarin ya faru ne a tsakanin watan Janairu zuwa Augusta.

Kamfanin na UPS dai ya ce, kodayake bai samu wasu rahotanni ba na yin amfani da bayanan da aka sata don yin wata zamba, yakamata abokan huddarsa su rinka sa ido a kan asusun su, ga duk wasu harkoki na kutse.

Karin bayani