Taron tsaro kan ta'addanci a Afirka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyoyi irinsu al-shabab a Somalia da Boko Haram a Afirka ta yamma na ci gaba da yi wa zaman lafiya a Afirka barazana

Manyan hafsoshin tsaro a Afrika suna ganawa a Nairobi babban birnin kasar Kenya domin tattauna hanyoyin da za a bullo wa masu tsattsauran ra'ayi a nahiyar.

Ana sa ran tattaunawar ta tsawon mako guda za ta bullo da hanyoyin musayar bayanan sirri da kuma nazarin hanyoyin da za a bullo wa Kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai irinsu al-shabab da Boko Haram wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci da miyagun laifuka.

Farfesa Bube Na-maiwa a jami'ar Anti Diop da ke Senegal ya ce karuwar masu tsaurin ra'ayi a kasashen Afirka na da alaka da talauci da kuma rashin kula wajen sauke nauyin gwamnatoci a kan 'yan kasa musammam ta fuskar samar da aikin yi ga Matasa da suka kammala karatu.

Ya ce Matasa sukan kasance cikin bacin rai idan sun kammala karatu amma Hukumomi ba su tanadar musu abin yi ba.

Farfesa Na-maiwa ya ce wajibi ne a sauya manhajar kasashen Afirka da aka gada daga wajen 'yan mulkin mallaka don ta dace da yanayi da tsarin kasashen nahiyar.

Ya ce kamata ya yi Hukumomi su shigar da sarakuna cikin harkokin tsaro, don kuwa su ne ke kusa da jama'a, kuma su ya kamata su dinga sa ido a kan shigi da ficen baki.