An tsige mataimakin gwamna kan kiwon Kaji

Image caption Gwamnatin jihar Enugu ta ce babu ruwanta a cikin wannan batu na tsige mataimakin gwamna

Majalisar dokokin jihar Enugu a kudu maso gabashin Nijeriya ta tsige Mr Sunday Onyebuchi saboda kiwon kaji a fadar gwamnati.

A kwanakin baya ne mataimakin gwamnan ya bayyana a gaban wani kwamitin bincike da aka kafa, inda majalisar ta tuhume shi a kan kiwon kaji ba bisa ka'ida ba a gidan gwamnati, a matsayin daya daga cikin laifukan da ake zargin ya aikata.

Sai dai wasu bayanai na nuna yatsa ga gwamnan jihar, a kan zuga majalisar dokokin wajen tsige Mr. Sunday Onyebuchi, zargin da gwamnatin Enugu ta sha musantawa.

Mutane da dama a Nijeriya, na bayyana mamaki kan yadda kiwon Kaji zai kasance musabbabin tsige mataimakin gwamna, duk da kaurin suna da kasar ta yi kan ayyukan cin hanci da rashawa.