Amurka ta ce an shammace ta a Libya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikicin birnin Tripoli ya kazance a 'yan kwanakin nan

Jami'an Amurka sun ce Masar da Daular Larabawa sune ke da alhakin hare-haren nan da aka kai ta sama a kasar Libya a makon da ya wuce.

Wani jami'in Amurkar ya shaidawa BBC cewar ba a tuntubi Amurka ba kafin a kai harin an kuma shammace ta.

An ba da rahoton cewar hare-haren da aka kai ta sama a Tripoli babban birnin Libyar Daular Larabawa ce ke da alhakin kai shi kuma ta yi amfani ne da filayen jiragen sama ne dake kasar Masar.

Hukumomin kasar Masar dai sun musanta hannunsu a harin, kuma babu wani wanda yace uffan kai-tsaye daga daular ta Larabawa.

Amurka da kawayenta 4 na Tarayyar Turai sun yi tir da abinda suka bayyana cewa tsoma baki ne na wata kasar waje a harkokin kasar Libya.