Agwagin Madagascar na fuskantar barazana

Image caption Sune tsuntsayen da ba a cika ganinsu ba a duniya

Masana muhalli a Burtaniya sun ce agwagin Madagascar wadanda sune tsuntsayen da ba a fiye ganin irinsu ba a duniya na bukatar sabon wuri idan har ana son su rayu a doron kasa.

Agwagin da yawansu bai kai 30 ba, yanzu haka ne suka rage a daji a wani tafki mai nisa a arewa maso gabashin Madagascar.

Masu binciken sun gano cewa yankin da agwagin suke ba ya dauke da isashen abinci ga tusntsayen wadanda suke mutuwa yayinda suka kai makonni biyu zuwa uku a duniya.

Kashi 96% ne ke mutuwa a makonni biyu zuwa ukun kamar yadda binciken ya nuna.

An wallafa wannan bincike ne a mujallar Bird Conservation International.