Jiragen Amurka za su fara leken asiri a Syria

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption Amurka na son raunana masu tsattsauran ra'ayin 'yan Sunni, ba tare da ta taimaka ma Shugaba Assad ba.

Manyan jami'ai a Amurka sun ce Shugaba Obama ya ba da umurnin a yi amfani da jiragen yaaki na leken asiri a sararin samaniyar Syria don samun bayanai a kan kungiyar nan ta 'yan jihadi dake yunkurin kafa daular Musulunci.

Jami'ai a ma'aikatar tsaron Amurkar sun ce Mr Obama ya amince da amfani da jiragen ne na leken asiri a karshen mako.

Masu aiko mana labarai sun ce yunkurin zai iya zama matakin farko na fara kai hari ta sama kan wasu wurare a cikin kasar ta Syria

To amma babban abin damuwar fadar gwamnatin Amurkar shine yadda za ta raunana masu tsattsauran ra'ayin 'yan Sunni, ba tare kuma da taimaka ma Shugaba Assad ba.

Gwamnatin Syriar ta ce, a shirye take ta ba da hadin kai wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin.