Ebola: An dage ranar komawa makaranta

Malam Ibrahim Shekarau, ministan ilmin Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumomin Najeriya na daukar matakan kariya daga cutar Ebola har a makarantu

Ma'aikatar ilimi a Najeriya ta dage ranar komawa makarantu ga daliban Firamare da na Sakandare na gwamnati da masu zaman kansu na kasar baki daya.

An dai dage komawar zuwa ranar 13 ga watan Oktoba.

Ma'aikatar ilmin ta ce ta yi haka ne saboda daukar matakan kariya game da cutar Ebola.

Ministan lafiya na Najeriyai dai ya ce a yanzu mutum daya ne kachal ya rage da kwayar cutar.