An soki hotunan ban-tsoro a Facebook

Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Wasu hotunan datse kan mutane a Syria da aka sa a Facebook sun tada kura

Daya daga cikin mashawartan Facebook zai yi kira ga shafin da ya kirkiro da wasu matakai na tsaro domin hana masu amfani da shi daga cin karo da hotuna na ban-tsoro.

Wannan mataki ya biyo bayan korafe korafen da akai ta yi game da wasu hotuna da aka sanya a shafin dake nuni yadda aka datse kawunan mutane a wani bangare na kasar Syria dake karkashin ikon mayakan Islama na IS.

Kamfanin Facebook da farko dai ya ki ya goge hotunan, yana mai cewa basu saba da dokokin shafin ba.

Daga baya ne ya rufe hotunan bayan da BBC ta tuntube shi.

Stephen Balkam babban jami'i a wata cibiyar dake kula da tsaron iyali a shafin Intanet dake kasar Amurka, ya ce yana shirin tayar da wannan batu a wata mai zuwa, a wani taro da Facebook zai shirya na kwamitin dake bashi shawarwarin tsaro, wanda kuma yana daya daga ciki.

Ya na da ra'ayin cewa kamata ya yi a ce sai mutum ya kai shekaru 18 kafin ya kalli irin wadannan hotuna ko kuma bidiyo.

Mr. Balkam ya soki Facebook a bara bayan da yai watsi da kiraye kirayen da akai masa na ya goge wani bidiyo dake nuna wata mata ana datse mata kai a Mexico.

A wancan lokacin Facebook ya sanya wani gargadi ne takaitacce, daga bisani kuma ya cire bidiyon.