Kwale-kwale ya kife a Najeria

Rahotanni daga jihar Kogi a Najeriya na cewa wani kwale-kwale ya yi hadari kuma mutane da dama sun rasa rayukansu.

Karamin kwale-kwalen da ke daukar mutane hamsin ya yi hadarin ne ne a kogin Takande.

Igiyar ruwa ce ta ja shi a daidai wurin da aka yi taho mu gama tsakanin jirgin ruwan dakarun tsaro da ke sintiri a kogin da kuma na masu satar mai da suka cika nasu kwale-kwalen da gangunan danyan mai.

Har yanzu dai babu iya adadin wadanda suka rasu a hadarin.

Sai da wasu bayanai na cewa an gano gawarwaki hudu na wasu da suka rasu a hadarin kuma yanzu haka ana cigaba da aikin ceto don gano sauran mutanen da suka bace.

Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA a Najeriyar ta ce jirgin yana dauke ne da mutane sama da arba'in.