'Jan aiki a gaban Nuhu Ribadu'

Image caption Nuhu Ribadu ne ya yi wa jami'yyar adawa ta ACN takarar Shugaban kasa a 2011

Rahotanni na cewa wasu daga cikin gwamnonin Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria sun soma yunkurin hana tsohon shugaban EFCC, Malam Nuhu Ribadu zama dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP a jihar Adamawa.

Wasu jaridun Nigeria sun ruwaito cewar gwamnonin PDP sun soma takun saka tsakaninsu da wasu mukarraban Shugaba Goodluck Jonathan wadanda ake zargin su ne ke kokarin baiwa Malam Ribadu tikitin zama dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Adamawa da za a yi a watan Oktoba.

Bayanai sun nuna cewar wasu daga cikin gwamnoni su na zargin Nuhu Ribadu na iya kasancewa sojan gona na jam'iyyar APC mai adawa, a yayinda wasu kuma ke kallonsa a matsayin wanda ba za a iya juya shi ba.

Ribadu ya bar jami'yyar APC ne ya koma PDP inda ake zargin cewar ya sauya shekar ne bisa alkawarin cewar PDP za ta tsayar da shi takarar gwamna a zaben da za a yi ranar 12 ga watan Oktoba.

Tun a lokacin Ribadu ya musantan cewar ya shiga PDP ne don an yi masa alkawarin tikitin takarar gwamnan jihar Adamawa.

Wasu daga cikin wadanda ke kokarin samun takarar gwamnan a karkashin jam'iyyar PDP a zaben na jihar Adamawa sun hada da mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Umaru Fintiri da Buba Marwa da Markus Gundiri da kuma Ahmed Ali Gulak.