Taron Kasa: Me aka cimma ne ?

Image caption Shugaba Jonathan ne ya kaddamar da taron

Wakilai 500 daga sassa daban-daban a Nigeria sun kammala tattaunawar tsawon watanni biyar game da tsarin siyasa da makomar wannan kasa da ta ga munanan rikice-rikice tsakanin kalibunta masu yawa, addainai da yaruka.

Ma'aikacin BBC, Abdullahi Tasiu Abubakar ya yi nazari kan nasarar da taron tattauna makomar kasar ya cimma.

Yayin da gwamnatin Nigeria ta fara yunkurin aiwatar da shawarwarin taron kasar, 'yan kasar da dama na tambayar shin kwalliya ta biya kudin sabulu?

Kwararru kuma na tambaya a kan samun karbuwar wasu shawarwari har a aiwatar da su.

Wakilan taron, da suka fito daga dukkanin yankunan kasar, kuma suka wakilci muradan al'ummomi da suka sha bambam, sun tafka muhawara kan batutuwan da suka hadar da tsarin rabon arzikin kasa mai yawan janyo ce-ce-ku-ce da kuma tsarin siyasar kasar mai haddasa rarrabuwar kawuna.

Haka zalika, sun zartar da kudurori fiye da 600, inda suka fitar da wani rahoto mai shafi 10,335 wanda kuma aka gabatar wa shugaban kasar Goodluck Jonathan, inda shi kuma ya yi alkawarin aiwatarwa.

'Karin hadin kai'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan da Mai Shari'a Idris Kutigi

Jonathan ya fada wa shugabannin taron cewa "Za mu aika da bangarorin shawarwarinku ga Majalisar kasa da kuma majalisun dokoki don shigar da su cikin kundin tsarin mulki."

Shugaban taron, tsohon babban Joji na kasar Idris Kutigi, ya ce fargabar cewa taron ka iya zama sanadin wargajewar Nijeriya ta kau, ya ce an gudanar taron kasa lafiya, kuma kan 'yan kasa ya kara hadewa fiye da a kowanne lokaci.

'Wasu shawarwari'

  • Rushe tsarin kananan hukumomi 774 na yanzu don tattalin kudade da rage cin hanci. Jihohi suna iya kafa tsarin kananan hukumominsu.
  • Kirkiro sabbin jihohi 18, da za a raba daidai wa daida a fadin kasar. Jihohin da suke so suna iya hadewa waje guda idan sun cika wasu sharudda.
  • Rabon arzikin kasa, inda za a rage kason da ke shiga hannun gwamnatin tarayya tare da kara wa jihohi kaso.
  • Gyara tsarin shugaban kasa mai cikakken iko zuwa tsarin da ya kunshi shugaban kasa da gwamnatin majalisa, inda shugaban kasa zai dauki mataimakinsa daga Majalisar dokoki.
  • Raba ikon shugabanci da kuma yin karba-karba a kowanne matakin gwamnati.
  • A dinga karba-karbar kujerar shugaban kasa tsakanin arewa da kudu da kuma tsakanin shiyyoyi shida na kasar.
  • Kujerar gwamna wadda za a dinga karba-karba a tsakanin shiyyoyi uku na kowacce jiha.

Alfanu?

Shugaban wakilan yankin arewa Alhaji Ibrahim Coomassie ya ce duk abun da suka yi, sun yi ne don hada kan Nigeria a matsayin kasa guda, takwaransa na kudu, Cif Edwin Clark kuma ya ce "Mun zo taro, mun kammala kuma mun yi nasara."

Image caption Wasu na kallon taron a matsayin bata lokaci

Sai dai yayin da shugaban kasar da wakilai ke barka a kan abun da suka gani na nasarar taro, wasu kuma watsi suka yi da shi a matsayin wata dabarar karkatar da hankula da barnata dukiyar kasa.

Sun ce rashin tunani ne gudanar wannan taro watanni kalilan gabanin babban zabe na kasar a shekara mai zuwa, ana tsaka da rikicin 'yan tada-kayar-baya na Boko Haram mai neman durkusar da kasar.

Rahotannin rikicin 'yan tada-kayar-baya da cutar Ebola da ta barke a kasar cikin watan Yuli sau da yawa sun mamaye batutuwan taron.

Sakamakon taron, ya ma fi ba da kafa ga masu sukarsa, wadanda ke cewa ya gaza cimma muradun masu neman sake fasalin kasar.

Haka kuma bai gamsar da muradan wadanda suka fi kaunar ganin sauyi a tsarin kasar na yanzu ba, akwai ma tambayar matsayin taron a idon doka daga wasu wakilai.