Yarinya ta kashe mai koya mata harbi

Hakkin mallakar hoto Mohave County Sheriff
Image caption Koya wa yara harbi da bindiga a abu ne ruwan dare a sassan Amurka da dama

Wata yarinya ta harbe wani mai koya mata harbi da karamar bindiga mai sarrafa kanta a jihar Arizona ta Amurka.

Hatsarin ya faru ne lokacin da bindigar samfurin Uzi ta kwace daga hannun yarinyar 'yar shekara tara ta kuma ci gaba da sarrafa kanta.

Lamarin da yasa harsashi ya samu mai koyar da ita Charles Vacca, mai shekaru 39 a ka kuma ya mutu bayan an kai shi asibiti.

Yarinyar dai na tare da iyayenta ne a wajen koyon harbin kuma iyayen na daukar hoton bidiyo a lokacin da abin ya auku.