FBI na bincike akan hare haren satar bayanai

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumar bincike a Amurka FBI ta ce tana binciken wasu rahotannin da kafafen watsa labarai a kasar suka yada a game da hare-haren kutsen satar bayanai daga kwamfutocin wasu bankunan kasar.

Rahotannin sun nuna cewa wadanda suke satar bayanan, sun yi hakon bankuna biyu zuwa biyar ne a Amurkan, wadanda suka hada da shahararren bankin JP Morgan .

Bankin JP Morgan bai fito kai tsaye yayi magana akan al'amarin ba, amma dai ya ce manya-manyan kamfanoni irin sa a Amurka suna fuskantar hare-haren kutsen satar bayanansu a kwamfutoci a kowacce rana.

Hukumar binciken ta FBI ba ta bayyana ko su wanene take zargi da alhakin satar bayanan ba.

Cikin wata sanarwa, hukumar ta ce tana aiki da hukumar leken asiri na Amurka domin tantance girman kutsen.

Tashar watsa labarai ta Bloomberg wadda ta fara yada labarin harin kutsen cikin kwamfutocin bankunan ta ce a binciken da ake gudanar wa, ana duba yiwuwar hannun kasar Rasha a cikin al'amarin.

Hakan kuwa, ya na zuwa ne a daidai lokacin da dangartaka ke kara tsami tsakanin Rashan da Amurka saboda rikicin Ukraine da na kasashen gabas ta tsakiya.

Tashar ta Bloomberg ta tsinkayi wasu kwararru a fannin tsaro suna cewa ilimi da kwarewar da akayi amfani da su wurin kusten satar bayanai cikin wurare masu tarin tsaro, ya nuna cewa masu alhakin al'amarin ba kanana ba ne.

Sai dai tambayar da wasu sukeyi ita ce, ta yaya kutsen zai tsaya ga satar bayanai kawai, a maimakon gurbata yadda ayyuka ke gudana, da za a iya kallo a matsayin ramako daga wasu kasashe ga abin da Amurkan ta yi musu.

''Wannan ya sha banban da hare-haren kutsen da akayi zargin kasar Iran tayi a 2012 da kuma karshe-karshen 2013, na hana aiki tafiya,'' inji babban jami'in bangaren fasaha na kamfanin samar da tsaro na Imperva, Amichai Shulman.

Ya ce''nayi mamaki a ce mutumin da ya iya kutsawa cikin kwamfutocin banki amma ba yayi hakan bane domin ya ci moriyar shi anan''.

''Kowa yana kokarin alakanta al'amarin da takun saka tsakanin Amurka da Rasha. Amma ba abune boyayye ba a 'yan shekarunnan, ana yawan samun hare-haren kutse cikin kwambutocin bankuna daga gabashin turai don satar bayanai'', inji Shulman.