Karin mutane biyu sun kamu da Ebola

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chukwu ya ce Nigeria na kokarin rage yaduwar cutar Ebola

Wani likita a birnin Fatakwal na jihar Ribas a Nigeria ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Ebola.

Wannan shi ne karo na farko da wani dan kasar ya rasu a wata jihar da ba Lagos ba sakamakon cutar Ebola da ta bulla a kasar a ranar 25 ga watan Yuli.

Ministan Lafiya a Nigeria, Onyebuchi Chukwu ne ya bayyana haka a taron maneman labarai a Abuja.

Ministan ya kara da cewar a kuma samu karin mutane biyu dauke da cutar ta Ebola a Nigeria, kenan adadin masu dauke da cutar a kasar sun zama mutane 15.

Likitan wanda ya rasu, ya na daga cikin wadanda suka yi wa wani jami'in ECOWAS magani bayan ya yi mu'amala da dan Liberia Patrick Sawyer wanda ya shigo da cutar Ebola a Nigeria.

A yanzu haka mutane shidda ne Ebola ta hallaka a Nigeria.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce kawo yanzu mutane 1,552 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo da kuma Nigeria.

Karin bayani