Jonathan ya kaddamar da sabon katin dan kasa

Hakkin mallakar hoto Ruben Abati
Image caption Shugaba Jonathan aka soma baiwa katin shaidar zama dan kasa

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya kaddamar da karbar katin shaidar zama dan kasa wanda za a iya amfani da shi ta fuskoki daban-daban.

Hukumar kula da shaidar 'yan kasa watau NIMC wadda ke aikin samar da katin, ta ce ko baya ga zamansa shaidar zaman dan kasar, 'yan Nigeria na iya amfani da katin wajen saye da sayarwa da hada-hada a bankuna da karbar albashi ko tallafi daga gwamnati.

Bayan da shugaban ya karbin nasa katin, ya yi amfani da shi wajen ciro kudi daga wata naurar banki kuma ya sayi wata komfutar hannu wato Ipad da shi.

Hajiya Hadiza Ali Dagabana, Darakta mai kula da sa ido da kuma tabbatar da bin kai'doji a hukumar ta NIMC ta ce akwai gajiya da dama da za a samu daga amfani da katin.