Boko Haram: Najeriya ta samu tallafi

Wata makaranta da aka kai wa hari a Najeriya
Image caption Wata makaranta da aka kai wa hari a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu taimako na miliyoyin daloli daga gwamnatocin kasashe da kuma daidaikun mutane domin tallafa wa shirinta na samarda tsaro a makarantun da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Ministan watsa labaran Najeriyar Mista Labaran Maku ya ce daga cikin kasashen da suka tallafa wa shirin na Safe School Initiative har da Burtaniya wadda ta ba da tallafin Fam miliyan biyu kwatan kwacin Naira miliyan dari biyar.

Ya kuma ce Norway ta bayar dala milyan daya da rabi, bankin raya kasashen Afrika ya bada dala miliyan daya, yayinda shugaban bankin ya bada gudumuwar dala dubu hamsin.

Mr Maku ya kuma ce gwamnatin Jamus za ta bayar da euro miliyan biyu.

A tsakiyar watan Yuni ne dai shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da shirin domin samar da tsaro a makarantun yankin arewa maso gabashin kasar bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun afkawa makarantar 'yan mata a garin Chibok na jihar Borno inda suka yi awon gaba da dalibai sama ga dari biyu da har yanzu ba a ji duriyarsu ba.