'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun juya baya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Kiir da madugun 'yan tawaye Riek Machar

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun yi watsi da yarjejeniyar da aka sanya ma hannu a baya baya nan ta kafa gwamnatin hadin gwiwa da za ta kawo karshen wata da watannin da aka kwashe ana zubar da jini a rikicin kasar.

'Yan tawayen sun ce yarjejeniyar wadda, kungiyar kasashen gabashin Afrika ta IGAD ta jagoranci kullawa, ta tilasta a dora shugaba Salva Kiir ya ci gaba da kasancewa kan karagar mulki, har zuwa karshen wa'adin da aka diba na gwamnatin rikon kwarya.

Watannin da aka kwashe ana tashin hankali ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, wasu kuma sama da miliyan guda da dubu dari takwas an raba su da muhallansu.

Jagoran wakilan 'yan tawaye a tattaunawar, Taban Deng Gai ya ce su ba sa cikin wadanda suka amince da yarjejeniyar wadda ta ba dukkan bangarorin biyu, kwanaki arba'in da biyar na su kafa wata gwamnatin rikon kwarya wadda za ta shafe shekaru biyu da rabi tana mulki.

A karkashin wannan yarjejeniya wadda aka sa ma hannu a kasar Ehiopia mai makwabtaka da Sudan ta Kudun, 'yan tawayen ne zasu mika sunan mutumin da suke so a nada mukamin Firaminista wanda za a kirkiro.

Karin bayani