'Yan kasuwar Filato sun maka gwamnati a Kotu

Gwamna Jonah Jang na Filato Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Kasuwar yankin Terminus har yanzu na killace

Dubban 'yan-kasuwa a birnin Jos na jihar Filaton Najeriya sun kai gwamnatin jihar kara a gaban kotu suna bukatar kotun ta hana gwamnatin rusa kasuwar yankin Terminus.

A watan Mayun da ya gabata ne aka kai harin bama-bamai a kasuwar abinda ya janyo asarar rayuka da kuma dukiyoyi

'Yan kasuwar sun ce suna bukatar kotun ta tilsta gwamnatin sake bude masu kasuwar wadda ta killace tun bayan harin bama-baman.

Gwamnatin dai na shirin rusa kasuwar ne saboda a cewar ta, ginin kasuwar bai da nagartar da mutane za su iya zama a ciki sakamakon girgiza shi da ta ce bama-baman sun yi.

Sai dai 'yan kasuwar na cewa wannan hujja da gwamnati ke bayarwa babu gaskiya a cikin ta.

A ranar Laraba ne dai 'yan kasuwar suka shigar da karar a wata babbar kotu dake birnin Jos.