NATO: Sojojin Rasha sun shiga Ukraine

Hoton sojojin Rasha ta tauraron dan Adam Hakkin mallakar hoto c
Image caption Hoton sojojin Rasha ta tauraron dan Adam

Kungiyar tsaro ta NATO tace dakarun kasar Rasha kimanin dubu daya ne ke taya mayaka 'yan aware masu goyon bayan Rashar fada a gabashin Ukraine.

Kungiyar ta NATO ta kuma fitar da wasu hotunan tauraron dan adam da ta ce an dauke su ne a makon da ya gabata, dake nuna tankokin yakin kasar Rasha, kayan yaki ta sama ana shigar da su kasar Ukraine.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon,ya ce ya kadu game da samun rahotannin kazantar rikicin a gabashin Ukraine.

Mai magana da yawunsa Stephane Dujarric, ya ce Mr Ban yayi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su ci gaba da tattauwar diplomasiyyar da aka fara kan rikicin a farkon makon nan.

Karin bayani