Rasha na taimakon 'yan tawayen Ukraine

Image caption 'Yan tawaye ne ke iko da gabashin Ukraine

Jagoran 'yan aware masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine Alexander Zakhar-chenko, ya ce sojojin kasar Rasha na cikin dakarun da ke fafatawa da sojojin gwamnatin Ukraine.

A cewarsa, 'yan tawayen na da 'yan asalin kasar Rasha kusan dubu uku zuwa hudu, da ke taya su fadan, sun kuma hada da sojojin Rashar da suka yi murabus.

Kalaman nasa na fitowa ne yayinda jakadan kasar Ukraine, Geoffrey Pyatt ke zargin dakarun kasar Rashar da kasancewa da hannu dumu-dumu cikin rikicin dake faruwa.

A wani taron kungiyar lura da harkokin tsaro ta nahiyar Turai OSCE a Vienna, jakadan kasar Ukraine a kungiyar ya zargi kasar Rashar da hannu kan ricikin da ke faruwa.

Karin bayani