'Yan Boko Haram sun kwace garin Dikwa

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Shekau ya ce sun kafa daular Musulunci a Gwoza

Rahotanni daga garin Dikwa da ke jihar Borno a Nigeria sun nuna cewar 'yan Boko Haram sun kwace garin sannan suka kafa tutocinsu.

Bayanai sun ce 'yan Boko Haram dauke da manyan makamai sun shiga garin a ranar Alhamis da yamma sannan suka yi ta abubuwan da suka ga dama, ba tare da fuskantar wata tirjiya ba.

Wasu mazauna garin Dikwa da suka tsere sun tabbatarwa BBC cewar a yanzu haka garin yana hannun 'yan Boko Haram.

Garin Dikwa shi ne na baya-baya da 'yan Boko Haram suka kwace, baya da Gwoza da Limankara da Gamborou Ngala da , Ashgashiya, da sauran wasu kauyuka da garuruwa da ba a tantance ba, da ake cewa yanzu haka su ma suna karkashin ikon kungiyar.

Jaridar Daily Trust a Nigeria ta wallafa cewar Shehun Dikwa, Shehu Muhammad Masta II Ibn Alamin Elkanemi ya fice daga fadarsa tare da sauran iyalansa sakamakon diran ma garin da 'yan Boko Haram suka yi.

Duk garin da 'yan Boko Haram suka kama, suna kafa tutocinsu sannan a bar wani kwamanda a matsayin shugaba ko kuma Amir na garin.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ayyana yankin Gwoza a matsayin daular Musulunci bayan da suka kori jami'an tsaro.

Gwamnatin Nigeria ta yi watsi da ikirarin Boko Haram inda ta ce ba za ta bar wani yankin kasar ya kasance karkashin 'yan ta'adda ba.