Ebola: Liberia za ta dage takunkumi

Hakkin mallakar hoto
Image caption An samu hatsaniya tsakanin jami'an tsaro da jama'ar unguwar West Point saboda takunkumin

Gwamnatin Liberia ta ce, za ta dage takunkumin hana shiga da fita da ta sanya wa al'ummar wata unguwar talakawa da ta rufe, domin hana yaduwar cutar Ebola.

Ministan watsa labarai na kasar, ya ce za a bude unguwar ta West Point ne, saboda kwarin guiwar da suke da shi yanzu cewa za a iya yaki da bazuwar cutar yadda ya kamata.

Can kuma a Senegal, ministar lafiya ta kasar, Awa Marie Coll Seck, ta tabbatar da samun wani mutum da ke dauke da kwayar cutar ta Ebola, a karon farko a kasar.

Ta ce, '' wani matashin dalibi ne dan Guinea na wata jami'ar Conakry, wanda ya zo a duba lafiyarsa a asibiti, dauke da kwayoyin cutar amma bai yi tsanani ba.''

A halin da ake ciki kuma, masana kimiyya, sun ce sun gano cewa maganin cutar na gwaji mai suna Zee-Mapp, ya yi tasiri kashi dari bisa dari a jikin wasu birrai 18.

Sai dai har yanzu ba a kai ga tantance tasirinsa a jikin dan adam ba.