Gwamnatin Libya ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fraiminista Abdullah al-Thani

Gwamnatin rikon kwaryar Libya da Fraiminista Abdullah al-Thani ke jagoranta, ta mika takardar murabus dinta ga majalisar dokokin kasar.

A wata sanarwa da ta bayar, gwamnatin rikon kwaryar ta ce ta yi hakan ne domin bai wa majalisar damar kafa gwamnatin da za ta wakilci dukkanin al'ummar kasar.

Majalisar dokokin Libyan dai ta koma da zama a birnin Tobruk da ke gabashin kasar, saboda dalilai na tsaro.

Kungiyoyin mayaka na fafutukar kwace iko da babban birnin kasar, Tripoli, wanda ya fada cikin rikici.