Za a rufe MSN Messenger a China

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption MSN ta kawo sauyi ga yadda matasa ke sada zumunci cikin sauki da sirri.

Za a rufe hanyar sada zumunci da aikawa da sakonnin kar-ta-kwana ta kamfanin Microsoft, wato MSN Messenger a China a watan Oktoba, bayan shekaru 15.

A 1999 aka samar da MSN din, amma a 2013, an rufe ta ga akasarin masu amfani da ita bayan kamfanin Microsoft ya saye Skype da ke gogayya da MSN.

Har yanzu mutane a China suna amfani da tsohuwar hanyar sada zumuncin ta MSN Messenger, amma daga ranar 31 ga watan Oktoba, za a mai da su kan Skype.

A 2009, anyi kiyasin akalla mutane miliyan 330 ne ke amfani da MSN wadda kuma ake kira Windows Live.

Sai dai adadin mutanen da ke amfani da hanyar sun ragu daga baya, yayin da masu amfani da Skype su ka karu zuwa kusan miliyan 300 a 2012.

A 2005 ne aka fara amfani da Skype a China, amma daga baya Skype din ya fuskanci matsananciyar gogayya daga wasu shafukan intanet na China da suka hada da QQ Messenger da kamfanin Tancent ya samar.

Wata jaridar China ta ce da yawa daga cikin masu amfani da MSN Messenger a kasar sun samu sakonnin Email daga Microsoft a ranar Alhamis, inda aka sanar da su shirye-shiryen rufe MSN.

Jaridar ta ce kamfanin na Microsft ya sanar da masu amfani da MSN cewa za a ba su damar yin amfani da Skype kyauta idan suka yi hijira daga MSN zuwa Skype din.

MSN Messenger ya fara ne a matsayin hanyar sada zumunci da kananan rubutattun sakonni a 1999, inda yayi gogayya da hanyoyin sada zumunci na AOL's, AIM da ICQ.

Daga baya da aka kara samun ilimin akan hanyar ta MSN, sai aka kara bunkasa ta ta yadda za a iya aikawa da sakonni ta hotuna da kuma bidiyo da wasu wasanni na nishadi.

Saye hanyar sada zumunci ta Skype akan kudi dala biliyan takwas da rabi da kamfanin Microsoft ya yi a 2012, ita ce sila ta rufe MSN.

Dave Lee, na BBC, ya ce MSN ta yi tasiri sosai wajen sa mutane su lakanci rubuta sakonni cikin sauki kuma atakaice da kuma aika su cikin hanzari.

Sauran hanyoyin sada zumunci da za a cigaba da amfani da su bayan an rufe MSN sun hada da Facebook, MySpace, Twitter, Snapchat, Skype, Google+ da Instagram