PDP ta daga wa Ribadu da Marwa kafa

Image caption Nuhu Ribadu na fuskantar matsin lamba

Jami'yyar PDP mai mulkin Nigeria ta daga kafa ga 'yan takara uku da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar daga APC domin neman tsayawa takarar gwamnan jihar Adamawa.

Sanarwar da jami'ar PDP ta fitar ta ce a yanzu tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu da Janar Buba Marwa da kuma Markus Gundiri za su iya shiga zaben fitar da gwani na takarar PDP a zaben gwamnan Adamawa da ke tafe.

Wannan matakin da PDP ta dauka ya nuna cewar Malam Nuhu Ribadu na daga cikin mutane 11 da jam'iyyar PDP za ta tantance kafin zaben fitar da gwanin.

Tun daga shigar Malam Nuhu Ribadu cikin PDP aka soma tada jijiyar wuya tsakanin 'yan PDP wadanda suke zargin cewar ya sauya sheka ne bisa alkawarin zai zama dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Adamawa.

A ranar 11 ga watan Oktoba ne hukumar zaben Nigeria INEC ta ce za a gudanar da zaben gwamnan jihar Adamawa sakamakon tsige Gwamna Murtala Nyako da majalisar dokokin jihar ta yi.

Karin bayani