Rabin al'ummar Syria sun bar gidajensu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta koka akan yadda kasashen duniya ba sa taimaka wa 'yan hijirar Syria miliyan 3

Majalisar Dinkin duniya ta ce, sama da al'ummar Syria miliyan uku ne suka gudu daga kasar, domin tsira daga yakin da ake yi a kasar.

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar ta ce, rikicin na Syria, shi ne, rikici mafi muni da ya jefa mutane cikin halin kaka-ni-ka-yi a wannan zamani, amma kuma duniya ta kasa taimaka wa 'yan gudun hijirar da kasashen da suka ba su mafaka.

Hukumar ta ce, da dama daga cikin wadanda suka tseren, suna cikin mawuyacin hali, na tsoro da galabaita, inda kuma ba su da wani isasshen kudi.

Hukumar ta kara bayani da cewa, akwai kuma wasu karin miliyan shida da rabi na al'ummar Syrian da suka tsere daga muhallansu suke warwatse a cikin kasar, wanda hakan ke nufin kusan rabin al'ummar kasar, sun tsere daga gidajensu.