Baranzanar ta'adanci a Birtaniya

Ed Miliband Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jagoran 'yan adawa Ed Miliband

Jagoran 'yan adawa a Burtaniya Ed Miliband ya yi kira da a bullo da wani shirin dole na sauya tunanin duk wanda aka shigar cikin akidar tsatstsauran kishin Islama a kasar.

A wata kasida da ya rubuta a jaridar Independent, Mr Miliband ya ce a kwai bukatar a dauki tsauraran matakai na hana mutane zuwa Iraki da Syria don taya mayakan kungiyar fafutukar kafa daular musulunci fada.

Firaiminsta David Cameron ya ce kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci ita ce babbar barazanar tsaro da Burtaniya ke fuskanta fiye da ko wacce kungiya a baya.

Tun farko cibiyar hadaka ta nazarin ta'adanci ta kara matsayin karfin barazanar ta'adanci zuwa matakin da ya fi tsanani a karo na biyu saboda barazanar da yan burtaniya da suka dawo da ga yankin Su ke yi.