Ukraine: Muna dab da kaiwa makura

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce shugabannin tarayyar Turai sun amince da shirya azawa Rasha sabon takukumi , saboda hannun da take dashi kan rikicin dake faruwa a gabashin Ukraine.

Yayinda yake magana bayan ganawar shugabannin kungiyar ta EU a birnin Brussels, Mr Poroshenko ya ce aiwatar da hakan ya danganta ga sakamakon tattaunawar da za a yi a Minsk game da rikicin ranar Litinin.

Ya kuma kara da cewa yana fatan wannan zai haifar da cimma nasarar tsagaita wuta, amma halin da ake ciki yanzu ya kazanta.

"Ya ce ina jin muna gab da kaiwa makura. Kai wa ga makura yaki ne gadan gadan da ya riga ya faru a yankin da 'yan aware suke rike da iko".

Shi ma shugaban hukumar tarayyar Turai José Manuel Barroso,ya ce rikicin dake faruwa tsakanin kasashen Ukraine da Rasha ya kara kazanta, zai kuma iya kaiwa yadda ba za a iya cimmasa ba.

Karin bayani