Rasha na fuskantar karin takunkumi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Angela Merkel da shugabannin Turai

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta ce kungiyar tarayyar Turai za ta sanya wa Rasha karin sabbin jerin takunkumi, muddin rikicin gabashin Ukraine bai yi sauki ba.

Da take magana bayan taron shugabannin kungiyar a Brussels, shugabar ta Jamus, ta ce cikin mako daya kacal ne, za a dauki matakin sanya sabbin jerin takunkumin.

Shi kuwa shugaban Ukraine, Petro Poroshenko, cewa ya yi yanayin takunkumin da za a sake sanya wa Rashan, zai dogara ne ga sakamakon taron da za su yi da wasu jami'an Rashan, a Belarus, a mako mai zuwa.

Mr Poroshenko, ya yi gargadin cewa idan aka gaza kawo karshen tashin-tashanar ta yanzu, to kuwa ba shakka lamarin zai kai ga, cikakken yaki.

A halin da ake ciki kuma, Kungiyar Tarayyar Turan, ta zabi Firaiministan Poland, Donald Tusk, a matsayin sabon shugaban majalisarta, inda zai maye gurbin Herman Van Rompuy.

Yayin da ministar harkokin wajen Italiya, Federica Mogherini, za ta gaji Catherine Ashton, a matsayin babbar jami'ar harkokin wajen tarayyar Turan. .