Dakarun Somaliya sun kai hare-hare

Somalia troops Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Somaliya

Jami'an gwamnatin Somaliya sun ce dakarunsu wadanda ke samun goyon bayan dakarun tarayyar Turai sun kaddamar da wasu hare-hare akan mayakan kungiyar al-Shabaab da ke kudancin kasar.

Suna kai hare-haren ne domin kama wasu garuruwa biyu Buulo Mareer da kuma Baraaetwo dake yankin Lower Shabelle.

Gwamnan yankin da ke Lower Shabelle Abdulkadir Mohamed Nur , ya ce dakarun gwamnati na samun gagarumar nasara a hare-haren da suke kaiwa wadanda aka fara tun a daren Jumma'ar da ta gabata.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba