Matan Yazidi 300 ne aka sace a Iraqi

Mata mabiya addinin Yazidi a Iraqi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mata mabiya addinin Yazidi a Iraqi

Mata mabiya addinin Yazidi 300 ne da mayakan kasar Musulunci a arewacin Iraqi, aka tafi dasu kasar Syria aka sayar a matsayin ganima.

Kungiyar sa ido kan kare hakkin biladama ta kasar Syria ta ce tana rike da rubutattun shaidun irin yadda ake sayar da matan a matsayin matan 'yan kungiyar kasar musuluncin.

Ana kuma sayar da su kan kudi dala dubu ko wannensu, bayan an tilasta musu shiga addinin musulunci.

Ta ce duk wani yunkurin da masu fatan alkahairi ga Larabawa da Kurdawa suka yi na su sake sayen matan don yantar dasu ya gagara.

Kungiyar ta yi Allah wadai da batun sayar da matan, da ta ce tamkar wata haja.