An kashe mutane da dama a Gamborun Ngala

Yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan gudun hijira

Waso rahotanni daga garin Gamborun Ngala na jihar Borno da ke iyakar Najeriya da Kamaru na cewa, 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane dama a garin.

Rahotannin dai na cewa ne 'yan kungiyar sun rika bi suna tilastawa sauran mutanen da suka rage a garin na Gambourn Ngala, ko dai su dauki makami su shiga aikin kungiyar ko su kashe su.

Wasu mazauna garin sun shaida BBC cewa da farko 'yan Boko Haram sun fada masu cewa zasu iya zama garin ba zasu taba su ba sai dai daga bisani su ka sauya shawara

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin mazauna garin na Gamborun.

Daman tun a makon da ya gabata ne 'yan Boko Haram din suka kama garin a yunkurinsu na kafa daular musulunci.

Lamarin ya sa mutane da dama barin gidanjensu inda suke samun mafaka a garin Fotokol da ke Kamaru.