Israila za ta kwace Filaye a gabar Yamma

Hakkin mallakar hoto EPA

Isra'ila ta ba bada sanarwar shirinta na mallake kadada kusan dari hudu a yankin Paladinawa dake gabar yamma da kogin Jordan.

An yi amanna cewa wannan shine zai zama kwace mafi girma a cikin shekaru 30.

Gidan rediyon Isra'ila ya ce matakin, wani martani ne kan sacewa da hallaka wasu matasan Yahudawa a yankin cikin watan Yuni.

Mazauna yankin sun ce suna fatan raya filin, da mahukuntan Palasdinawa suka ce ke da dashen bishiyoyin 'yayan zaitun.

Mai magana da yawun shugaban Palasdinawa Ahmad Sukar ya ce wannan mataki zai kara sa halin da ake ciki ya kara munana.

Ya ce'' mun yi matukar mamaki da sanyin safiyar yau, lokacin da gwamnatin Isra'ila da rudunar sojinta suka yi gargadi tare da saka alamu a wurare da dama a yankunan Wadi Fukin.

Karin bayani