Mutane 10 sun mutu a wani hari a Somalia

Mayakan kungiyar al-Shabaab na kasar Somalia
Image caption Mayakan kungiyar al-Shabaab na kasar Somalia

Harin da aka kai kan helkwatar tsaro ta farin kaya a Mogadishu babban birnin Somalia ya hallaka mutane 10, tare da jikkata wasu.

Mahukunta sun ce bakwai daga cikin wadanda suka mutun mayakan al-Shabaab ne da suka tuka motar dake shake da ababan fashewa cikin harabar ginin.

'Yan bindigar dai sun yi kokarin shiga cikin ginin ta karfi.

Kungiyar ta al-Shabaab ta ce ta samu nasarar sakin fursunoni da dama daga cikin helkwatar dake da wuraren tsare fursunonin na karkashin kasa.

Wani wakilin BBC ya ce an yi ta jin karan musayar wuta a cikin harabar ginin, ya kuma ga motocin daukar marasa lafiya na diban gawawwaki daga wurin da lamarin ya faru.