Hafsoshin sojin kungiyar Ecowas na taro a Ghana

Taron manyan Hafsoshin sojin Ecowas Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron manyan Hafsoshin sojin Ecowas

A kasar Ghana an bude wani taro na yini uku na manyan hafsoshin sojojin kasashen kungiyar yankin yammacin Africa ta Ecowas karo na talatin da hudu.

Manyan abubuwan da taron zai duba dai sun hada da yadda za'a shawo kan cutar Ebola da tuni ta hallaka mutane akalla dubu biyu a wasu kasashe na yankin da kuma matsalar tashe tashen hankula da ya hada da rikicin Boko Haram a arewacin Nigeria.

A halin da ake ciki kuma hukumar Lafiya ta duniya ta ba da rahoton cewa yawan masu harbuwa da cutar Ebola na karuwa sosai a shiyyar Afirka ta yamma.

Ta ce kusan rabin adadin sama da mutum dubu biyu da dari biyun da cutar ta halaka, sun mutu ne a cikin makwanni ukun da suka wuce.

Hukumar ta yi gargadin cewa wasu dubban mutane ka iya harbuwa da cutar Ebola a kasar Liberia, inda annobar ta fi kamari.

Saderio Bellizzi, wani Likita ne da ke aikin yaki da cutar a kasar Liberia:

Ya ce,"lamarin ya munana. Akwai bukatar gadajen jinya akalla dubu daya da dari biyu. a halin da ake ciki gadaje dari biyu da arbi'an ake da su a Monrovia. mutane da dama kan zo kofar asibiti, haka muke cewa su koma gida, inda watakila a karshe mutuwa za su yi."