Kananan kasashe sun haskaka a rahoton Mo Ibrahim

Mo Ibrahim Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mo Ibrahim

A nan London an fitar da rahoton shekara shekara na Mo Ibrahim kan kyakykyawan shugabanci a Afrika.

Rahotan dai na auna nagartar shugabanci ne da kuma bunkasa jama'a a kasashen Afrika.

Kamar a ko da yaushe dai rahoton na bana ya kunshi komai da komai, inganci da kuma rashinsa.

Galibi a kan kasance da zumudi a daidai wannan lokacin game da ko wa zai lashe kyautar Shugabancin ta Afrika.

mutumin da ya kirkiri kyautar, wato dan kasuwar nan haifaffen Sudan, Mo Ibrahim, ya bayyana cewar kasashe irisu Mauritius da Afrika ta Kudu da Namibia da Seyschilles na gaba gaba wajen tabuka abun azo a gani na ci gaban kasa da kuma bunkasa rayuwar jama'a.

Mr Mo Ibrahim ya ce kasashe irinsu Najeriya matsalar boko haram a arewacin kasar da kuma cin hanci da ya ce mutane sun dade suna magana kansa

Sai dai ya ce duk da kokarin da gwamnati ke cewar tana yi matsalar ta cin hanci ta ci gaba da zama tamkarcutar sankara a Najeriya.

Amma kuma ya ce karfin halin yan Najeriya ya sa duk da haka suna sa yalwar tattalin arzikin kasar na dorewa.