Kungiyar EU ta kara kakaba takunkumi kan Rasha

Takunkumin Eu a kan Rasha Hakkin mallakar hoto Getty

Jakadun kasashe wakilan Kungiyar tarayyar Turai da ke taro a Brussels sun cimma yarjejeniya a kan sabon takunkumin tattalin arzikin da za su sanya wa kasar Rasha.

Sun dai yanke shawarar cewa sabon takunkumin zai fara aiki ne nan da wasu kawanaki.

An cimma yarjejejniyar ne lokacin da kasar Finland ta nemi a yi mata bayani dalla-dalla ko za a cire takunkumin idan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a gabashin Ukraine ta dore, inda kasashen suka ce suna iya sauya matsayi idan yarjejeniyar ta yi karko.

Kasar Finland dai ta dogara ne da kasar Rasha wajen samun iskar gas.