Mutane da dama sun mutu a rikicin Wukari

Sifeto Janar din 'yan Sandan Nigeria Hakkin mallakar hoto Nigeria Police
Image caption Sifeto Janar din 'yan Sandan Nigeria

Rahotanni daga jihar Taraba dake arewa maso gabashin Nijeriya na cewa akalla mutane goma sha daya sun rasa rayukansu, wasu fiye da arba’in kuma suka jikkata a wani sabon tashin hankali mai nasaba da kabilanci da addini da ya barke da jijjibin asubahin Talata.

An kuma kona dukiya mai dimbin yawa a tarzomar wadda ita ce ta baya-bayan nan a jerin rigingimu da jihar ta Taraba ke yawan fama da su musamman a kananan hukumomin Wukari da Ibi.

Bayanai dai na cewa tashin hankalin ne a lokacin da garin ya rude da rugugin manyan bindigogi, kana kone-kone suka biyo baya.

Malam Audu Ali daya daga cikin shugabannin Hausawa da Fulani Musulmi a garin na Wukari, ya ce sun yi imanin 'yan kabilar Jukun mabiya addinin Kirista ne suka fara harbe-harbe abin da ya yi sanadiyar barkewar rigimar.

Sai dai daya daga cikin shuagabannin 'yan kabilar Jukun, Mista Zando Hoku, ya musanta hannun Jukunawa a harin, kana ya ce sun yi imanin wasu 'yan tsiraru ne ke neman kara dagula lamaura tsakanin musulmi da kirista a garin bayan da aka fara samun fahimtar juna.

Nigeriya dai, baya ga rigingimu masu nasaba da Boko Haram dake mata tarnaki, a baya-bayan nan wata babbar matsalar tsaro da kasar ke fuskanta ita ce ta yawan fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini, inda baya ga a jihar Taraba, akan kuma yi fama da irin wadannan rigingimun a jihohi kamar Kaduna da Filato da Benue.

Ko a makon jiya mutane da dama ne aka bada labarin suka rasa rayukansu a wani tashin hankalin tsakanin Fulani makiyaya da 'yan kabilar Eggon a jihar Nasarawa.

Karin bayani