Nigeria: matar likita ta kamu da Ebola

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane shida cutar ta Ebola ta hallaka a Nigeria

Matar wani likita da Ebola ta kashe a Fatakwal ta jihar Rivers a Najeriya ta kamu da kwayar cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar Sampson Parker, ya ce, bincike ya nuna matar wadda mijinta dakta Ike Enemo ya rasu ranar 22 ga watan Agusta sakamakon kamuwa da Ebola, ta harbu da cutar.

Mijin nata ya kamu da cutar ne bayan da ya yi jiyyar wani ma'aikacin kungiyar ECOWAS, wanda yayi mu'amulla da Patrick Sawyer dan Liberia da ya kawo cutar Najeriya.

Sai dai ma'aikatar lafiya ta jihar Lagos, ta ce an dawo da matar Lagos, ana kula da ita a wata cibiya ta masu fama da cutar.

Hukumomi sun binciki mutane sama da 200 da suka yi mu'amulla da matar.

Wannan shi ne karon farko da cutar ta Ebola ta yadu a wajen jihar Lagos.

Karin bayani