'Yan Boko Haram sun kama garin Bama

Image caption Dakarun na fuskantar matsi daga Boko Haram

A Najeriya, rahotanni daga jahar Borno da ke arewa-maso-gabashin kasar na cewa 'yan bindiga sun kwace iko da gari Bama, bayan an shafe tsawon wunin yau ana fafatawa tsakanin wasu da ake zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne da kuma sojojin Najeriya.

Sai dai wasu rahotanni sun ambaton hedikwatar tsaron Najeriya na ikirarin cewa sojoji sun sake kwace garin daga hannun mayakan 'yan kungiyar boko haram.

Sai dai mutanen da ke fitowa daga garin sun ce 'yan Boko Haram din sun kwace shi.

Bayanai sun nuna cewar 'yan Boko Haram sun aukawa garin ne da asubahin yau Litinin.

Wani jami'in tsaro da bai son a ambaci sunansa, ya ce duk da cewa sojojin Najeriya sun yi kokari waje kare garin na Bama, amma zuwan jirgin sama da ya kawo dauki ya sa su ma sojojin suka ranta a na kare, saboda jirgin ba ya iya tantance dan duma da kabewa, wato ba ya warewa tsakanin 'yan Boko Haram da sojojin Najeriya.

Kodayake wasu majiyoyi na ganin watakila ya kai hari barikin ne don lalata makaman da sojin suka tara a wurin, don a hana su fadawa hannun 'yan Boko Haram.

Garin Bama shi ne na baya-bayan nan da 'yan Boko Haram suka kaddamar hari a kai, inda akan yi asarar rayuka da ta dukiya mai yawa.

Rahotanni sun nuna cewar, kungiyar Boko Haram ta kafa tutocinta a garuruwan Gwoza, Madagali, Liman Kara, da Gamborou Ngala da kuma Ashgashiya da sauransu.

Garin Bama na da tazarar kilomita kusan 72 daga Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.