'Yan Boko Haram sun kai hari a Bama

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Abubakar Shekau ya ce babu gudu babu ja da baya

Rahotanni daga garin Bama a jihar Bornon Nigeria sun nuna cewar 'yan Boko Haram sun kai hari da manyan makamai a yunkurin da suke yi na ci gaba da kwace garuruwa a arewa maso gabashin kasar.

Garin Bama shi ne na baya-bayan nan da 'yan Boko Haram suka kaddamar hari tare da barnata dukiyoyin jama'a.

Bayanai sun ce mutane da dama sun tsere daga garin domin kaucewa fadawa cikin tarkon Boko Haram.

Garin Bama na da tazarar kilomita kusan 40 daga Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno.

Rahotanni sun nuna cewar kungiyar Boko Haram ta kafa tutocinta a garuruwan Liman Kara, da Gamborou Ngala da kuma Ashgashiya.

Rikicin Boko Haram ya raba dubban mutane da muhallinsu.

Karin bayani